Likitoci a Maradi ta Jamhuriyar Nijar sun fadakar da iyaye mata su rika kwana a cikin gidan sauro saboda irin illar da cutar take yiwa mata masu juna biyu da kananan yara. Likitocin suna matukar fargaba cikin watannin Agusta da Satumba saboda lokaci ne da zazzabin cizon sauro yake kwantar da mata da kananan yara saboda faduwar damuna.
Kwamishinan yaki da cutar zazzabin cizon sauro cikin jiha Mohamman Lawali Jajuna ya bayyana cewa, binciken da suka yi ya nuna mutane dubu dari biyu da tamanin da takwas da dari uku da daya suka kamu da zazzabin cizon sauro daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu, cikinsu an sami sama da dari da suka rasu. Bisa ga cewarshi, masassarar cizon sauro tafi kama mata da kananan yara kasa da shekaru biyar.
Yace an sami kananan yaran da shekarunsu basu cika daya ba wadanda suke dauke da zazzabin cizon sauro dubu hamsin da biyar da dari biyar da tara, daga ciki talatin da biyar suka rasu.
Bisa ga cewarshi, an sami kananan yara tsakanin shekaru biyu zuwa biyar da suke dauke da cutar zazzabin cizon sauro, dubu dari da arba’in da dari da goma sha shida cikinsu yara saba’in da biyu suka rasu. An kuma sami mata bakwai da suka rasu sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro.
Kwamishin ya bayyana cewa, rashin kwana a cikin gidan sauro ne ya kawo yawan masu kamuwa da cutar da kuma mutuwa. Ya bayyana cewa, wadansu suna cire gidan sauron idan an basu, wadansu kuma maganin ya daina aiki amma har yanzu suna ci gaba da amfani da shi. Yace wadanda suke da gidajen sauron da maganinsu ya daina aiki, suna iya zuwa wurin likita a sake tsomawa a cikin maganin kyauta ko kuma suje su sake sayen wani domin kwana a cikin irin wannan gidan sauron bashi da amfani.
Wakilin Sashen Hausa Choibu Mani ya aiko da rahoton.