Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan Amurka a Najeriya Ya Gargadi 'Yan Najeriya


Yayin da ya kai ziyara jihar Filato, Jakadan Kasar Amurka a Najeriya James Entwisle ya gargadi 'yan Najeriya su rungumi zaman lafiya lokacin zabe da kuma bayan zabe.

Jakadan kasar Amurka a Najeriya ya gargadi 'yan Najeriya da kada su yadda da tashin hankali lokacin zabe da ma bayansa.

A wata ziyara da ya kai jihar Filato ya gana da dalibai da shugabannin jami'ar Jos inda yace makasudin ziyarsa shi ne karfafa batun tsaro da yadda daliban zasu fahimci mahimmancin zaman lafiya musamman a zaben 2015 dake karatowa. Jakadan ya kuma gargadi 'yan jarida akan su fi bada fifiko akan labaran zaman lafiya maimakon bada wadanda zasu rarraba kawunan mutane. Yace 'yan jarida suna da gagarumar rawa da zasu taka. Yace dalili kenan da yasa yana karfafa gidajen telebijan da na radiyo akan su bada himma wajen tattaunawa da 'yan takaran dake da niyyar cigaban kasa. Yace 'yan jarida na iya canza 'yan siyasa ta yadda zasu zama masu kishin kasarsu da kuma tallafawa talakawan da suka zabesu.

Shugaban jami'ar Jos Farfasa Hayward Mafuyai yace duk da matsalolin tsaro kamar su Boko Haram da sace sacen jama'a da matsalar fyade da sauran muggan dabi'u da Najeriya ta fada ciki yana da tabbacin cewa za'a shawo kan matsalolin. Yace Najeriya zata cigaba da dogaro akan tallafin gwamnatin kasar Amurka domin shawo kan matsalolin tsaro, zamantakewa da inganta tattalin arzikinta. Ya kuma yabawa kasar Amurka akan horonda take baiwa malaman jami'ar ta Jos.

Tun farko sai da jakadan ya ziyarci gwamnan jihar Filato Jonah Jang inda ya nuna takaicinsa akan matsalar dake tsakanin manoma da makiyaya musamman a yankin arewa ta tsakiya inda ya bukaci al'umma da su rungumi akidar zaman lafiya da juna. Yayin da yake mayarda martani gwamnan Filato yace duk da matsalar da kasar ke fuskanta yana da tabbacin cewa Najeriya zata yi fice wajen zama zakara a harkokin dimokradiya a Afirka da duniya baki daya. Gwamnan yace sun gudanarda zaben kananan hukumomi cikin zaman lafiya kuma cikin gaskiya domin haka ana samun cigaba.

Ga rahoton Zainab Babaji
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG