Kashe matasan ya jawo cecekuce da tada jijiyoyin wuya domin jama'ar kasar da dama basu yadda da ikirarin jami'an tsaro ba. Bugu da kari wasu 'yanuwan wadanda aka kashe sun fito suna karyata batun. Ban da haka kunyiyar keke napep ta kalubali jami'an tsaro inda tace wadanda aka kashe 'ya'yan kungiyarta ne kuma har ta nuna katunan shaida nasu.
Kungiyar keke napep ta dauki lauya domin ya taimaketa. Haka ma ita hukumar kare hakin biladama ta gudanar da bincike mai zurfi. Chidi Odinkalu shugaban hukumar ya bayyana sakamakon binciken. Yace hukumar bata samu matasan da laifi ba. Saboda haka samamen da jami'an tsaro suka kai ya keta hakinsu lamarin da ya kaiga rasa rayuka takwas da raunata goma sha daya. Ya nemi a biya diyar nera miliya goma goma ga duk wadanda aka kashe kana a a biya nera miliyan biyar biyar ga wadanda aka raunata.
Usman Buba Goza shugaban kungiyar keke napep a Abuja yace ya fi kowa farin ciki da hukuncin domin sun nemi gwamnati ta daina kiransu 'yan Boko Haram kuma hakan ya faru. Shi ma Barrister Solomon Dalung lauya mai kare hakin biladama yace hukuncin ya kwantar masa da hankali. Yace an yi adalci. Yace yanzu an kama hanyar kwatarwa jama'a hakinsu daga jami'an SSS.
Ga rahoton Medina Dauda.