Dokar hana fitar ta haddasa cutar amai da gudawa da ake zaton kwalara ce. Ban da cutar akwai kuma rashin samun abinci da ruwan sha.
Kakakin gwamnan jihar Taraba Mr. Kefas Sule yace sakamaakon bullar cututuka da kuncin rayuwa da mazauna garin suka samu kansu ciki yasa gwamnati ta sassauta dokar. Yanzu mutane na iya fita daga karfe takwas na safe zuwa karfe goma sha biyu na rana. Yace an ba mutane sa'o'i hudu su samu su fita su nemi abinci. Wadanda kuma basu da lafiya su samu su nemi magani.
Kakakin gwamnatin jihar yace ba'a so a janye dokar gaba daya domin gudun kada wani abu ya faru. Yace za'a duba a ga yadda lamarin zai wakana kafin a yi tunanin watakila a kara lokacin fita zuwa sa'o'i takwas. Za'a ci gaba da yin haka kafin a janye dokar gaba daya.
Wani da aka zanta dashi a garin Ibi yace har yanzu cutar amai da gudawa na zagayawa kuma akwai karancin magani. Duk shagunan dake sayarda magani suna rufe ko kuma basu da maganin sam.
Sanadiyar dokar rahotanni na cewa mutane tara sun rasa rayukansu kana wasu da dama suna fama da amai da gudawa. Amma gwamnatin jihar tace tana kokarin kai karin magunguna domin taimakawa wadanda suka kamu da ciwo. Mukaddashin gwamnan jihar ya bada kudi a sayi magunguna a akai garin na Ibi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.