Masu kushe neman kirkiran 'yan sandan jiha, karkashin gwamnoni na ganin 'yan siyasa ka iya mayar da su tamkar 'yan banga ne masu bindiga.
Tsohon sufeton janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Kumasi na ganin inganta martabar 'yan sandan ne mafita ga dawo da doka, da oda.
Ibrahim Kumasi yace “Police an riga an maida ta mace, ba abinda akeyi sai a zo, a kirkiro wata kungiya, a bata aikin Police kuma a basu kudi, a basu kayan aiki. Ita kuma Police, ta nanan inda take, mu zamu bada shawara tsakanin mu da Allah.”
Mr. Kumasi ya kara da cewa “tun shekarar 2009 ake ta kashe-kashe, tun daga wajen boko haram har ta kai yanzu ma, bamu san shin boko haram ne ke kashe mutanenmu ba, ko kuma wasu ne daban?”
Banda fargabar amfani da irin wadannan 'yan sanda ba bisa ka’ida ba, wasu na ganin haka ma na iya karawa masu rajin dawo da batun kafa kasar Biafra kwarin gwiwa.
Ikwe Martins wanda shima yake hallartar taron na ganin wannan bahagon tunani ne, har yake cewa “muna sa addu’a, inshaAllah siyasar da sunaso su kawo a taron, ba zai yi tasiri ba. Kasar nan, an haifai mu daya, kuma zamu mutu inshaAllahu mu bar kasar daya.”
Martins ya kara da cewa “in dai talauci, talauci ne a kudu, talauci ne a arewa, in an ce rashin aiki ne, rashin aiki na a kudu, rashin aiki ne a arewa.”