Gwamnonin sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka nemi a janye dokar ta bacin kacokan a kuma sauya lale da yakin da ake yi da 'yan ta'ada.
Alhaji Ahmed Sajoh daraktan yada labaran gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya bayyana dalilan da gwamnonin suka bayar na son a janye dokar. Yace idan har dokar ta baci bata cimma burinta ba bayan shekara daya to kamata yayi a sauya salo. Watakila sauya salon ka iya kaiga nasara. Abubuwan da suka faru cikin shekara daya yakama su zama darusan da zasu kaiga samun maganin ta'asar da a keyi ba lallai sai an sake sabunta dokar ba.
Haka kuma gwamnonin sun nemi hukumar zaben kasa wato INEC tayi koyi da kasar Afghanistan wadda ta gudanarda zabe duk da barazanar da kungiyar Taliban tayi. Kungiyar tayi barazanar kai hari idan aka kuskura aka shirya zabe. Amma hukumar zaben kasar da gwamnatin kasar da talakawan kasar sun hada kai sun fito sun yi zaben. Yace mutane sun nunawa 'yantsagera cewa tsagerancinsu ba zai hana mutane kyautata rayuwarsu ba. Haka yakamata INEC da gwamnatin da al'ummomin kasar su yi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.