PM kasar Rasha ya kushewa shawarar da kungiyar hadin kan larabawa ta yanke na dakatar da aikinta na sa ido a kasar Siriya sakamakon tashin hankalin dake karuwa a kasar da kungiyoyin kare hakin bil’adama suka ce an kashe a kalla mutane 36 a wurare dabam dabam na kasar.
Kafar sadarwar kasar Rasha ta ambaci ta bakin ministan harkokin kasashen ketare na kasar Sergei Lavrov yau Lahadi yana cewa, a maimakon haka zai goyi bayan kara yawan masu sa ido a kasar.
Jiya ne babban magatakardar kungiyar hadin kan Larabawa Nabil Elaraby ya bayyana cewa, kungiyar ta yanke hukumcin daina aikin sa idon ne bayan tattaunawa da ministocin kasashen ketare na kungiyar suka yi. Ya dorawa gwamnatin kasar Siriya alhakin tashin hankalin dake kara ruruwa ya kuma bayyana cewa, wadanda abin yafi shafa farin kaya ne da basu ci ba basu sha ba.
An tsaida shawarar dakatar da aikin ne bayan wani hari da gwamnati ta kai a kewayen Damascus babban birnin kasar da kuma sauran birane da suka hada da Hama da Idlib da kuma Deir el-Zour. Hotunan bidiyo da ‘yan tawaye suka dauka ya nuna jirgin atilaren gwamnati na luguden wuta kan a kalla garuruwa shida, yayinda gwamnati da kuma yan adawa ke tsirawa juna hannu dangane wutar da ta tashi a wani bututun mai.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Siriya Mohammed al-Shaar ya bayyana jiya asabar cewa, za a ci gaba da murkushe masu zanga zangar har sai an raba kasar da bata gari da masu keta doka.
Jakadan kungiyar hadin kan Larabawa zasu gana cikin makon nan domin tsaida shawara kan aikin sa idon.