Mataimakin shugaban kasar china Xi Jinping ya gayawa shugabannin Amurka cewa a shirye kasarsa take “domin tattaunawa ta hakika” kan hakkin Bil-Adama, kuma yayi alkawarin China zata bada hadin kai kan harkokin da suka shafi tattalin arziki.
Xi yace ya jaddadawa shugaban Amurka Barack Obama da mataimakinsa Joe Biden a ganawarsa da suka yi a fadar White House jiya talata cewa, “China ta sami gagarumin ci gaba da hobbasawa ta azo a gani” dangane da mutunta hakkin Bil-Adama tun lokacinda ta fara aiwatarda sauye sauye. Duk da haka yace har kullum akwai damar kara ingantawa.
Da ya juya kan harkokin tattalin arziki da cinikayya, mataimakin shugaban kasa Xi ya gayawa mahalarta wata liyafar cin abinci da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta shirya masa cewa tilas Amurka da China suyi aiki sosai wajen ganin an cimma daidaito a fannin cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu, kuma su warware dukkan matsaloli da suka fuskanta ta yin shawarwari, ba kare kasuwanninsu ba.
Kalaman mataimakin shugaban kasan na China ya biyo bayan tabbacin d a shugaba Obama ya bashi cewa Amurka tana farin cikin ganin habakar China a duniya, duk da haka yace tilas ne dukkan kasashen duniya su mutunta dokoki dangane da tattalin arzikin duniya da kuma mutunta hakkin Bil-Adama.
Da yake karbar mataimakin shugaban kasan China a ofishin shugaban Amurka da ake kira ‘Oval Office’, shugaba Obama yace gagarumin ci gaba da China ta samu a cikin shekaru fiyeda ashirin da suka wuce, ya kawo mata bunkasa da karfi, wadda kuma yace ya “aza mata karin nauyi”.