Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Ce Tana Gina Sabuwar Mashigar Arewacin Kasar Don Kai Agaji Gaza


Sojojin Isra’ila
Sojojin Isra’ila

A yau Alhamis, sojojin Isira’ila sun sanar da abin da suka kira, sababbi matakai da aka inganta na shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, cikin har da gina wata sabuwar mashiga ta kasa a arewacin Gaza.

WASHINGTON, D. C. - Mai magana da yawun rundunar sojin Rear Admin, Daniel Hagari, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ta faifan bidiyo cewa, sabuwar mashigar za ta ba da damar samun Karin kayan agaji kai tsaye ga fararen hula a yankunan da ke fusakantar kalubale na shigar manyan motocin dakon kayan.

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun kwashe tsawon lokacin suna kokawa kan shingaye da aka saka na shigar da kayan agaji da manyan motoci zuwa Gaza, inda suka yi nuni da cewa,sojojin Isira’ila sun yi jinkiri da kuma rashin samun tsaro a wasu yankuna kamar arewacin Gaza, sakamakon barnar da yakin ya yi.

Hagari ya ce Isira’ila na sa ran manyan motoci 50 a kowace rana za su bi ta wannan sabuwar mashigar, kuma adadin manyan motocin da ke isa zirin Gaza a kowace rana sannu a hankali za su karu daga 350 zuwa kusan 500.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG