Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shagulgulan Easter: Paparoma Ya Yi Kira A Tsagaita Wuta A Gaza Da Ukraine


Vatican Pope Easter
Vatican Pope Easter

Miliyoyin mabiya addinin Kirista a fadin duniya na bikin Easter a yau Lahadi, wanda muhimmin lokaci ne da suke tunawa da tashin Yesu Almasihu bayan mutuwarsa.

A Fadar Vatican, Paparoma Francis ya gabatar jawabin da ya saba yi a duk shekara ga mabiya addinin Kirista a duk fadin duniya, inda ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza da Ukraine da duk wurare da ke fuskantar kalubale sanadiyar yaki.

Mabiya addinin Kirista a fadan Vatican yayin da Paparoma Francis ke jawabinsa na Easter na bana
Mabiya addinin Kirista a fadan Vatican yayin da Paparoma Francis ke jawabinsa na Easter na bana

Paparoma Francis ya kuma yi kira da a sake sauran Yahudawa da aka yi garkuwa da su yayin harin da aka kaiwa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

A Najeriya kuma, Rabaren Lawal Ibrahim Tsanyawa, yayin wata kebabbiyar hira da Muryar Amurka bayan nasa jawabain a jihar Kano, ya ce Easter lokaci ne na gudanar da aduo’i’n ga kasa da ma yan uwa baki daya, ya kuma kara da cewa, lokaci ne na bada kyaututtuka da sada zumunci.

Rabaren yayi adu’a da Allah ya sa shugabannin Najeriya su yi adalci sannan yayi riko da hannayensu wajen kamanta wannan adalcin da saukin rayuwa.

Muhimmancin Easter Tare Da Rabaren Lawal Ibrahim Tsanyawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Wasu mabiya addinin Kirista sun nuna jin dadinsu da ganin wannan rana inda suka nuna farin cikin tashin Yesu Almasihu daga matattu.

Sakonnin Wasu Kiristoci A Kano Game Da Ranar Easter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

A birnin Washington, Fadar gwamnatin White House na shirin gudanar da bikin nan da ake kira ‘Easter Egg Roll.’

Ana sa ran yara mutane kusan dubu 40, za su halarci bikin a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, wanda ya samo asali tun daga shekarar 1878.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG