Gwamnan Dalong ya nuna cewa akwai alamun budewar kofar yin zaben 'yar tinke ga jihar da ta ga za ta iya, ta hanyar amincewar akasarin shugabannin jam'iyya wanda zai bada damar a duba yiwuwar yin haka.
Sakataren jam’iyyar Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, ya bukaci jam'iyyar sa ta APC ta tabbatar da adalci wajen zaben fidda gwanin jam'iyyar ga masu son takarar mukamai a zaben 2019.
Da alamu gwamnoni sun yi nasarar ture matsayar farko ta shugabannin jam’iyyar na zaben 'yar tinke da takaita hakan ga zaben shugaban kasa kadai. Zaben fidda gwanin shugaban kasa na APC ba zai haifar da sabon abu ba fiye da gangamin jam'iyya a Abuja don jam'iyyar ta tsayar da shugaba Buhari a matsayin dan takara ba hammaya.
Mamban APC Mala Buni ya yi bayanin yadda lamarin yake, inda ya ce an gwada fidda gwani na gwamnan jihar Osun, ya ce don haka duk jihar da ke son 'yar tinke za ta iya nema a ba ta dama. Wasu 'yan takara na fargabar zaben fidda gwani ta hanyar wakilai saboda yin hakan zai ba wa 'yan amshin shatar gwamnoni ne nasara kawai, inda 'yan bora za su tashi a tutar babu.
Facebook Forum