Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Nijar Suna Aiki Tare Ta Fuskar Difilomasiyya Da Soja-Buratai


Janar Tukur Buratai ya kai ma sojoji ziyara a bakin daga cikin dajin Sambisa
Janar Tukur Buratai ya kai ma sojoji ziyara a bakin daga cikin dajin Sambisa

Hukumomin tsaro a Najerya sun tabbatar da cewa suna aiki kafa da kafada da takwarorinsu a jamhuriyar Nijar, don magance kusten 'yan binidga kan iyakokin kasashen biyu.

Leftanar Janar Tukur Buratai, babban hafsan mayakan kasa na Najeriya shine ya tabbatar da haka, yace tuni kasashen biyu suke aiki ta fuskar difilomasiyya data soja domin magance kutsen da 'yan binidga suke yi kan iyakokin kasshen biyu.

Idan za'a iya tunawa a shirin ranar Alhamis, Ministan tsaron jamhuriyar Nijar Kalla Moutari, yace dakarun kasshen biyu suna aiki tare ta wajen yin sintiri, domin magance 'yan binidgar masu neman kafa gindin zama akan iyakar kasar, watakil ganin yadda farmaki daga dakarun Najeriya ka iya korarsu su nemi tsallakawa zuwa Nijar.

Shima da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu,tsohon Gwamnan soja a jihohin kano da Benue,kanal Aminu Isa kontagora yace akwai bukatar a fadada rundunonin soja da suke aiki a jihohi da suke kan iyaka.

Shugaban hukumar wayar da kan al'uma ta Najeriya Dr. Garba Abari, yayi kira da jama'a su baiwa jami'an tsaro hadin kai domin a sami nasarar kawar da batagari.

Ga rahoton Hassan Maina kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG