Kamar yadda bayanai ke cewa lamarin ya faru ne a Maisamari, a wani shingen duba ababen hawa da ‘yan sanda suka kafa, inda sau tari ake zargin suna karbar na goro.
Kafa shingaye a yankin na Mambila an fara ne a shekarar da ta gabata bayan rikicin da ya faru na fadan kabilanci, wanda ya jawo asarar rayuka.
Sai dai kuma kamar yadda bincike ke nunawa, tun lokacin ne aka turo jami’an tsaro domin kare rayuka, to amma kuma sai wasu jami’an tsaron da aka ajiye su ka koma cin zarafin jama’a da karbar na goro.
A irin wannan yanayin ne wani jami’in dan sandan kwantar da tarzoma, ya harbe wani direba akan yaki bashi cin hancin Naira hamsin, kamar yadda suka saba karba a hannun masu kananan motoci, to amma fa shima wannan jami’in dan sandan daga bisani ya gamu da fushin jama’a bayan da ya gudu zuwa wani ofishin ‘yan sanda domin fakewa.
Wannan lamari dai yanzu haka ya tada hankalin sarakuna iyayen al’umma a yankin na Mambilla, Mai martaba Lamdo Nguroje, Alhaji Adamu A. Bairo, ya danganta abin da ya faru da abin takaici, kana ya shawarci jama’a da a kaucewa daukar doka a hannu.
Ya ce “Wannan abin takaici ne da ya faru. Gaskiya ba wanda yaji dadi domin ya tayar mana da hankali matuka. Kuma don Allah jama’a su guji daukar doka a hannu.”
Ya zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, bata yi cikakken bayani ba kan wannan batu, inda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ASP David Misal, ke cewa ana bincike, kuma ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani dan sandan da aka samu ya na karbar cin hanci, to amma kuma ya ce in bera na da sata ai daddawa na da wari.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum