Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijirar Najeriya Sun Sami Taimako


Jirgin 'yan Gudun Hijira
Jirgin 'yan Gudun Hijira

‘Yan gudun hijirar da suka hallarci wannan darasin da aka dauki tsawon mako guda a jihar Legas sun bayyana dalilan da suka sanya su kokarin tafiya turai domin neman sauyin rayuwa.

Mai Magana da yawun hukumar jin dadin ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, Paul Dillion, ya shaidawa Muryar Amurka cewa ‘yan gudun hijirar sun ba da labarin cin zarafi da wahalhalun da suka fuskanta a hannun ‘yan fasa kwabri a kasar Libiya.

Sannan wadanda suka dauki wannan darasi sun bayyana fatan su na samun nasara a gaba.

Wannan darasi shi ne karo na 21 tun da aka kaddamnar da shi a watan Afrilun shekarar 2017.

Kungiyar ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa ta bayyana cewa ‘yan Najeriya fiye da 2000 ne suka samu kammala wannan shiri wanda ake gudanarwa a jihohin Legas, Edo, Nassarawa, Kano da Kaduna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG