Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Buhari Zai Je Yi a China


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Masana tattalin arziki, na ganin China ta kasance kasa da ke zama barazana ga kasashen yammaci, wajen huldar kasuwancin da kasashen nahiyar Afirka, musamman ta fuskokin samar da ababan more rayuwa kamar wutar lantarki da fannin sufuri.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kama hanyarsa ta zuwa China a yau Juma’a domin halartar taron kolin hadin kan kasashen Afirka da Chinan t fuskar cinikayya.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa shugaba Buhari shawara kan yada labarai, Malam Garba Shehu, ta ce Buhari zai fara ganawa ne da ‘yan Najeriya mazauna kasar ta China, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ana kuma sa ran zai hadu da sauran shugabannin kasashen Afirka da takwaran aikinsa na China Xi Jinping a taron wanda zai mayar da hankali kan yadda za a karfafa dangantakar kasashen Afirka da kasar ta Sin.

Har ila yau ana sa ran zai gana da Jinping kan batutuwan cinikayya da ci gaban kasa da China da Najeriya suka saka a gaba.

Masana tattalin arziki, na ganin China ta kasance kasa da ke zama barazana ga kasashen yammaci wajen huldar kasuwancin da kasashen nahiyar Afirka, musamman ta fuskokin samar da ababan more rayuwa kamar wutar lantarki da fannin sufuri.

Halartar taron kolin na shugaba Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da ya karbi bakuncin Firai Ministar Burtaniya Theresa May da kuma shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a Abuja, wadanda duk suka tattauna da shugaban kan harkokin kasuwanci.

Shugabannin biyu sun kai ziyarar ce daban-daban.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG