Wasu mutane hudu, biyu daga cikinsu yara kanana sun rasa rayukansu, a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama kan wani sansanin tantuna na Al-Mawasi dake gabar teku, da aka ware a matsayin tudun mun tsira, sannan an hallaka wasu mutum 2 a wasu matsugunan wucin gadi dake birnin Rafah na kudancin zirin a harin jirgi maras matuki, a cewar jami’an kiwon lafiya.
A garin Beit Lahiya dake arewacin Gaza kuma, jami’an bada agaji sun ce makami mai linzamin da sra’ila ta harba ya fada kan wani gida, inda ya hallaka akalla mutane 2 tare da jikkata wasu da dama. A jiya Lahadi, ma’aikatan bada agaji da mazauna yankin sun ce harin Isra’ila ta sama akan wani bene a yankin ya hallaka gomman mutane tare da raunata da dama.
Rundunar sojin Isra’ila, wacce ta jima tana yaki da mayakan kungiyar Hamas a zirin Gaza tun a watan Oktoban 2023, tace ta kaddamar da hare-hare akan sansanonin ‘yan ta’addan dake Beit Lahiya.
Wani harin Isra’ila ta sama akan wani gida a birnin Gaza ya hallaka mutane 7 tare da jikkata wasu 10, a cewar jami’an bada agaji. Daga bisani a yau Litinin, harin Isra’ila akan sansanin Nuseirat dake tsakiyar zirin Gaza ya hallaka wasu mutane 4, kamar yadda suka kara bayyanawa.
Isra’ila dai bata ce uffan ba akan hare-haren na yau Litinin.
Ma’aikatar Lafiya Ta Gaza Tace Hare-Haren Sojan Isra’ila Sun Hallaka Falasdinawa 76 A Zirin Cikin Sa’o’i 24.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna