Jami'an Filasdinu sun ce wani farmakin da Isra'ila ta kai wani Massalaci a zirrin Gaza ya kashe akalla mutane 19.
A wani bangaren kuma, Isra’ila tana ci gaba da zafafa hare-haren ta a arewaci Gaza da kudancin Beirut a ranar Lahadi yayin da take fadada yakin ta da kungiyoyin masu kawance da Iran a fadin yankin.
Har yanzu Isra'ila tana fafatawa da Hamas a Gaza, shekara daya bayan harin bazatar da Hamas ta kai Isra’ila, sannan ta fara wani sabon yaki da Hezbollah a Beirut wacce take ta musayar wuta da Isra’ilar tun bayan fara yakin Gaza.
Isra’ila ta lashi takobin kaiwa Iran farmaki bayan da Tehran ta kai mata harin makamai masu linzami masu cin dogon zango a makon da ya gabata.
Rikicin da ke ci gaba da ruruwa yana iya sanya Amurka wace take baiwa Isra’ila mahimman tallafin soji da na diffolamasiyya, da kuma kasashen larabawa kawayen Amurka da suke baiwa sojojin Amurka wurin zama. Tuni kungiyoyin mayaka a Syriya, Iraq, da Yemen kawayen Iran suka sa hannu a rikicin da kai hari masu cin dogon zango Isra’ila.
Dandalin Mu Tattauna