Dakarun Isra’ila sun fadada hare haren su a arewacin Gaza, sannan sun kutsa kuryar arewacin birnin na Gaza da tankokin yaki, suna luguden wuta a wasu wurare a unguwar Sheikh Radwan, lamarin da mazauna suka ce ya tursasawa mutane da dama barin gidajen su.
Mazauna unguwar sun ce dakarun Isra’ila sun sanya shinge tsakanin Beit Hanoun, Jabalia da Beit Lahiya dake kuryar arewa da birnin Gaza, inda suka sanya shinge tsakanin yankuna 2, har sai mutanen da suke so su bi umarnin da aka basu su fita daga birnin da iyalan su sun nemi izini kafin su fice daga garuruwan 3.
Kwanaki 9 bayan da Isra’ila ta kaddamar da farmaki mai girma a arewacin Gaza, gwamnatin Hamas dake iko akan ofishin labarai a Gaza ta ce hare haren da Isra’ilar ta kai sun kashe akalla falasdinawa 300. Ta ce manufar Isra'ila ta lalata gidajen falasdinawa fararen hula da wuraren dake zaman mafaka da Isra’ila tayi itace don su tursasa mutane barin Gaza har abada, zargin da Isra’ila ta musa.
Mazauna Jabalia da dama sun wallafa a kafafen sadarwa cewa “Ba zamu tafi ba, zamu mutu sannan, baza mu tafi ba.”
Dandalin Mu Tattauna