Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Na Ci Gaba Da Luguden Wuta A Tsakiyar Gaza


Zirin Gaza, Yuni 9, 2024
Zirin Gaza, Yuni 9, 2024

Sojojin Isra'ila sun sake kai wani sabon hari a tsakiyar Gaza a jiya Lahadi, kwana guda bayan kashe Falasdinawa 274 a wani farmaki da suka kai da nufin ceto mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

WASHINGTON, D. C. - Haka kuma sun dada kutsawa da tankokin yaki a cikin Rafah a wani yunkuri na kewaye wani bangare na birnin dake kudancin kasar, in ji mazauna birnin da kuma kafar yada labaran Hamas.

Har yanzu Falasdinawa na cikin yanayin kaduwa saboda adadin mutanen da suka mutu a ranar Asabar, wanda shi ne mafi muni da aka gani cikin sa'o'i 24 a yakin Gaza da aka kwashe watanni ana yi, ciki har da mata da kananan yara da yawa in ji likitocin Falasdinu.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 274, adadin da ya karu daga 210 da ta sanar a ranar Asabar, yayin da wasu su 698 suka samu raunuka a lokacin da wasu kwamandojin Isra'ila na musamman suka kutsa cikin sansanin Al-Nuseirat mai cunkoson jama'a don ceto wasu mutane hudu da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su tun a watan Oktoba.

Ofishin yada labaran gwamnatin Gaza dake karkashin ikon Hamas ya sanar a ranar Lahadi cewa 64 daga cikin wadanda suka mutu yara ne yayin da 57 mata ne.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe wani jami'in soja na musamman a wata musayar wuta da 'yan tawayen, wadanda suka fito daga inda suka boye a wani rukunin gidajen zama, kuma sun san cewa an kashe Falasdinawa 'kasa da 100', ko da yake ba a san ko nawa ne mayaka ko fararen hula ba.

A ranar Lahadi bangaren sojan kungiyar Hamas ya ce an kashe wasu ‘yan Isra’ila uku da aka yi garkuwa da su, ciki har da wani dan kasar Amurka, a yayin farmakin da aka kai, amma ba a bayyana sunayensu ba. Kungiyar ta fitar da wani bidiyo da ya nuna wasu gawarwaki da aka sakaya fuskokinsu don kada a gane ko su waye.

Ikirarin da Hamas ta yi a ranar Asabar na cewa wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun mutu, sojojin Isra'ila sun yi watsi da shi a matsayin "karya".

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG