Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren Isra’ila A Zirin Gaza Ya Hallaka Akalla Mutane 17


Gaza, Yuni 18, 2024.
Gaza, Yuni 18, 2024.

Hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a ranar Talata sun hallaka akalla Falasdinawa a wasu sansanonin zirin gaza 2 masu tarihi, a yayin da tankokin Isra'ila ke kara kutsawa zuwa kudancin birnin Rafah, a cewar mazauna yankin da ma'aikatan lafiya.

Mazauna yankin sun ba da rahoton kazamin luguden wuta daga tankuna da jiragen saman yaki a yankuna birnin Rafah daban-daban, inda sama da mutane miliyan guda suka fake gabanin watan Mayu. Tun daga wancan lokaci al’ummar yankin suka arce zuwa arewaci a yayin da dakarun Isra’ila suka mamaye birnin.

Wani mazaunin Rafah kuma uban 'ya'ya 6 ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar, ana cigaba da yin luguden wuta akan rafah ba tare da samun dauki daga sauran duniya ba, kasar isra'ila dake mamaya na cigaba da cin karenta babu babbaka anan."

Tankokin Isra'ila na cigaba da ta'addanci a yankunan Rafah na Tel-Sultan da Al-Izba da Zurub harma da Shaboura dake tsakiyar birnin.

Kuma suna cigaba da mamaye yankunan gabashin yankin dama wajensa harma da kan iyakarsa da masar da kuma mashigar rafah mai mahimmancin gaske.

Hukumomin kiwon lafiyar Falasdinu sun ce bindigogin Isra'ila sun hallaka mutum guda a gabashin yankin Rafah da safiyar yau.

A cewar jami'an kiwon lafiya, an yi ittifakin cewar an hallaka wasu da dama a kwanaki da makonnin da suka gabata amma kungiyoyin masu ceto sun kasa kaiwa garesu.

Sun kara da cewar, rundunar sojin Isra'ila tace, tana cigaba da kai muhimman hare-hare bisa amfani da bayanan sirri a rafah, inda suka hallaka dimbin 'yan bindigar falasdinawa a fafatawar kusa da kusa tare da kwace makamai.

Kuma rundunar sojin saman Isra'ila ta yi nasarar kai dimbin hare-hare a fadin zirin na gaza.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG