Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Gabatar Da Shirin Tsagaita Wuta Na Kwanaki 135 Da Ficewar Isra'ila Daga Gaza


Kudancin zirin Gaza (Photo by SAID K
Kudancin zirin Gaza (Photo by SAID K

Hamas ta gabatar da shirin tsagaita wuta da a zirin Gaza na tsawon watanni hudu da rabi, inda duk wadanda aka yi garkuwa da su za su kubuta, Isra'ila kuma za ta janye sojojinta daga zirin Gaza sannan kuma za a cimma yarjejeniya kan kawo karshen yakin.

WASHINGTON, D. C. - Shawarar kungiyar ta Hamas, wadda martani ne ga tayin da masu shiga tsakani na Qatar da Masar suka aike a makon da ya gabata kuma Isra'ila da Amurka suka riga suka duba, na zuwa ne a dai dai lokacin da aka yi wani yunkuri na diflomasiyya mafi girma na tsawaita wutan.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken lokacin sadawarsa da Firai Minista kuma Ministan harkokin waje na kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani, a Annex, a Doha Fabrairu 6, 2024
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken lokacin sadawarsa da Firai Minista kuma Ministan harkokin waje na kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani, a Annex, a Doha Fabrairu 6, 2024

Kawo yanzu dai Isra’ila ba ta mayar da martini ba kan janye sojojinta daga Gaza ba har sai an kawar da Hamas.

Hamas dai ta yi hasashen zai dauki kwanaki 45 a samu maslahar kowani matsalolin uku. Mayakan za su yi musayar sauran mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga Oktoban shekarar da ta gabata ga fursunonin Falasdinu.

Za a fara sake gina Gaza, sojojin Isra'ila za su janye gaba daya, sannan a yi musayar gawarwaki da suaransu.

Sojojin Isra’ila a kusa da motar kasar Masar mai dauke da kayan agaji a kusa da Iyakar Kerem Shalom na Yankin Falasdina - Fabrairu 6, 2024
Sojojin Isra’ila a kusa da motar kasar Masar mai dauke da kayan agaji a kusa da Iyakar Kerem Shalom na Yankin Falasdina - Fabrairu 6, 2024

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya isa Isra'ila cikin dare bayan ya gana da shugabannin kasashen Qatar da na Masar masulhunta.

Wata majiya da ke kusa da masu tattaunawar ta ce matakin na Hamas bai bukaci a ba da tabbacin tsagaita wuta ba tun da farko, amma sai an amince da kawo karshen yakin a lokacin sulhun kafin a sako mutanen na karshe da aka yi garkuwa da su.

Qatar/US/Blinken
Qatar/US/Blinken

Ezzat El-Reshiq, mamba a ofishin siyasa na Hamas, ya tabbatar da cewa an mika wannan shawara ta hannun Qatar da Masar ga Isra'ila da Amurka.

Ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, "Mun yi matukar sha'awar tunkara da kyakkyawar ruhi don dakatar da kai hare-hare kan al'ummar Falasdinawa da kuma tabbatar da tsagaita wuta tare da samar da agaji, da taimako, da matsuguni da kuma sake gina kasar."

Falasdinawa da suka ji rauni ana kai su asibitin Shuhada al-Aqsa a Deir Al-Balah
Falasdinawa da suka ji rauni ana kai su asibitin Shuhada al-Aqsa a Deir Al-Balah

A cewar takardar, a cikin kwanaki 45 na farko, za a saki dukkan matan Isra’ila da aka yi garkuwa da su, maza ‘yan kasa da shekara 19 da kuma tsofaffi da marasa lafiya, domin a sako mata da kananan yara Falasdinawa daga gidajen yari na Isra’ila. Isra'ila kuma za ta janye sojojinta daga yankunan da ke da yawan jama'a.

Ba za a fara aiwatar da kashi na biyu ba har sai bangarorin sun kammala "tattaunawar kai tsaye kan bukatun kawo karshen ayyukan soji da kuma komawa cikin kwanciyar hankali."

Mataki na biyu zai hada da sakin sauran mazajen da aka yi garkuwa da su da kuma "Janye sojojin Isra'ila a wajen iyakokin dukkanin yankunan zirin Gaza."

Israel/Palestinians
Israel/Palestinians

A mataki na uku za a yi musayar gawawwaki da sauransu. Haka kuma tsagaita wutar za ta bar shigawar kayan abinci da sauran kayan agaji ga fararen hula na Gaza, wadanda ke fuskantar yunwa da karancin kayan masarufi.

Bayan wani hari na Isra’ila a Rafah
Bayan wani hari na Isra’ila a Rafah

"Mutane na da kyakkyawan fata, a lokaci guda kuma suna addu'a cewa wannan fatan ya zama yarjejeniya ta hakika da za ta kawo karshen yakin," Yamen Hamad, mahaifin 'yan hudu, wanda ke zaune a makarantar Majalisar Dinkin Duniya a Deir Al-Balah a tsakiyar yankin Gaza ne ya shaida wa manema labaran Reuters ta hanyar saƙo.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG