Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Babu Tabbacin Wa Zai Zama Shugaban Amurka


Kididdiga, lissafi da kuma ikirari iri iri na dada jefa ayar tambaya kan ko wa zai zama Shugaban Amurka na gaba.

Har yanzu akwai shakku game da wanda ya lashe zaben shugaban Amurka ya a yau dinnan. Lissafin sakamakon ya dogara ne kan wasu jihohi kalilan inda aka samu yawaitar akwatunan kuri’u da aka aika ta akwatin gidan waya saboda annobar coronavirus, da har yanzu ba a kidaya ba.

Shugaban Amurka Donald Trump da abokin hamayyarsa na Democrat, Joe Biden dukkansu sun ci jihohin da ake sa ran za su yi nasara a kokarinsu na samun rinjaye a kason kuri'un da ke tantance wanda ya lashe Shugabancin kasar a tsarin dimokuradiyya a kaikaice.

Amma sakamakon a jihohi da yawa – kamar North Carolina, Georgia da Pennsylvania a yankin gabashin kasar, Michigan da Wisconsin a tsakiyar yammaci, da Arizona a Kudu maso Yamma - ba a samu kwanciyar hankali ba yayin da jami'ai suka kidaya miliyoyin kuri'u, wasu kuma aka jefa a ranar Talata da karin da yawa a cikin makwannin jefa kuri'a da wuri.

Duk da rashin tabbas, Trump ya bayyana a gaban kyamarori a Fadar White House da safiyar yau Laraba ya na mai cewar ya yi imanin ya yi nasara kuma ya ce, zai je har Kotun Koli don kokarin dakatar da kidaya kuri’u.

Trump ya ce, "Wannan babbar damfara ce ga al'ummarmu," ya kara da cewa, "Kamar yadda na sani, tuni na yi nasara.

Gangamin yakin neman zaben Biden ya ce ikrarin da Shugaba Trump ya yi na cewa zai rufe kidayar kuri’un a matsayin “abin da bai kamata ba” kuma mataki ne na kwace wa Amurkawa hakkokinsu na zabin da suka yi na yin zabe kafin ranar kada kuri’a.

Tun da farko, Biden ya yi wa magoya bayan nasa jawabi a garinsa na Wilmington, Delaware, don yi musu godiya da kuma nuna kwarin gwiwar zai yi nasara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG