Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Biden Na Dakon Sakamakon Muhimman Jihohi


Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.
Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

Ana ci gaba da dakon sakamakon zabe na Muhimman Jihohi da 'yan takara a Zaben na Amurka Donald Trump dan Republican, mai neman wa'adi na biyu da Joe Bide na Jam'iyar Democrat, ke zawarcinsu don cin kujerar shugabancin kasa.

A daren jiya Talata aka rufe rumfunan zabe a fadin rabin gabashin Amurka yayinda Shugaba dan Republican Donald Trump da abokin hamayyarsa na Democrat, Joe Biden suke dakon sakamakon zabe na hukuma daga jihohin da suka kara sosai don shiga fadar White House a wa’adin shekaru hudu.

An fara rufe Rumfunan ne a jihar Indiana dake gabas ta tsakiya da Kentucky inda Trump ya samun nasara kamar yadda ake tsammani.

Dukka ‘yan takaran biyu suna ikirarin cin wasu jihohin kamar yadda ake zato, amma sakamakon jihohin fegen daga babu tabbas a wanna lokaci.

A yawancin jihohin kidayan kuri’u na mataki na farko farko inda kada kuri’u suka ci gaba saboda banbancin locaci a yammacin Amurka

Zaben 2020 a Kentucky
Zaben 2020 a Kentucky

*Sanata dan Republican wanda shine shugaban masu rinjaye ya koma don yin wa’adi na bakwai in da ya kada tsohuwar mai tukin jirgin yaki a sojin ruwa Amy McGrath.

*An samu layuka masu tsawo na masu jira su kada kuri’a a fadin Kasar kuma an samu rahoton wasu rumfunan zaben sun bude a makare.

*Jami’an tsaro na FBI sun ce suna binciken kiraye kiraye da aka yi na karyawa jama’a gwiwa a wasu jihohi. Amma ba’a samu tashin hankali mai yawa ba a rumfunan zabe kamar yadda wasu suka tsorata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG