Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasar Amurka


TRUMP da BIDEN
TRUMP da BIDEN

Da sanyin safiyar yau Talata masu kada kuri’a zasu fita zuwa runfunan zabe don zabar gwaninsu inda zasu jure layi mai tsawo don ganin sun yi amfani da ‘yancin da dokar kasa ta basu na zabar wanda zai shugabance su.

Miliyoyin Amurka ne suke kwarara zuwa runfunar zabe a fadin kasar domin yanke shawarar a kan ko shugaba Donald Trump na Republican ya ci gaba da shugabancin Amurka ko kuma a yi waje da shi a baiwa abokin takararsa na Democrat tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden damar mulkin kasar.

Kawo yanzu, sama da Amurkawa miliyan 97 suka riga suka kada kuru’unsu. Adadin da ya kai sama da kashi biyu cikin uku na kuru’un da aka kada a shekarar 2016 da mutum miliyan 139 suka kada kuri’a, inda Trump ya yiwa ‘yar takarar Democrat Hillary Clinton bazata ya doketa ya yi nasarar shiga fadar White House.

Masu zabe a Amurka
Masu zabe a Amurka

Ganin yanda wadanda suka kada kuru’u da wuri suke da dimbin yawa, ya sa ake harsashen cewawadanda za su kada kuri’a a zaben na shekara ta 2020 ka iya kai miliyan 150 ko fiye da haka, lamarin da ke zama tarihi a Amurka. Dokokin wasu jihohi a kan zaben aike yasa ba za a san adadin wadanda suka kada kuri’a da wuri ba sai yau Talata da dare ko kuma gaba kafin a samu sakamakon kuru’un aiken da aka kada.

Zaben shugaban kasar na zuwa bayan yakin neman zabe mai zafi da munanan kalamai daga masu takaran biyu Trump da Biden suna kokarin jan hankalin masu zaben. A ranar karshen da ya gudanar da yakin neman zabe domin fahimtar da masu zabe dalilin da yasa ya kamata su zabe shi ya ci gaba da mulki a wani wa’adin shekaru hudu, shugaban Amurka Donald Trump yace a wa’adin na biyu “zamu gyara harkoki a Washington kana zamu tsare tsinkayar Amurka.”

Shugaban ya nanata a jiya Litinin a jihar North Carolina cewa an samun bunkasar tattalin arziki a cikin wannan annobar coronavirus kana ya yi alkawarin raba maganin rigakafi a cikin ‘yan makwanni masu zuwa, duk kuwa da cewa, jami’an kiwon lafiya ciki har da wadanda suke tare da Trump sun ce akwai yiwuwar Amurkawa da dama ba zasu samu maganin a farko ko kuma tsakiyar shekarar 2021.

Shugaban Amurka Donald Trump a wurin yakin neman zabe
Shugaban Amurka Donald Trump a wurin yakin neman zabe

Trump ya fada a taron gangaminsa na farko a jiya Litinin cewa idan aka zabi abokin karawarsa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, zai maida kasar kurkuku karkashin dokar hana zirga zirga da zummar dakile cutar.

Shiko Biden ya fada a jiya Litinin a Cleveland dake jihar Ohio cewa matakin farko a yaki da wannan cuta shine yin waje da Trump.

Biden ya sha kushewa matakan da shugaba Trump ya dauka na yaki da cutar Coronavirus. Biden ya shaidawa wani taron ganganin yakin neman zabe cewa, ”

miliyoyin mutane sun rasa ayyukansu sabili da annoar, kuma basu ganin wani haske yayinda shugaba Trump ya karaya ya yi watsi da iyalanmu ya kuma daina yaki da cutar”

Tsohon mataikamin shugaban kasar Amurka Joe Biden a wajen yakin neman zabe
Tsohon mataikamin shugaban kasar Amurka Joe Biden a wajen yakin neman zabe

Biden ya ce zai “zabi kyakkyawar makoma a maimakon fargaba. Za mu zabi hadin kan a maimakon banbanci. Kimiyya a maimakon tatsuniya da kuma gaskiya a maimakon karya.”

Gabannin wannan rana ta yau, Shugaban Amurka Donald Trump da abokin hamayyarsa na jam'iyyar Democrat, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, sun ziyarci jihohin da ake yiwa lakabi da fagen daga, don karawa magoya bayansu karfin gwiwa kwanaki biyu gabanin zaben kasa na yau Talata don neman wa’adin shekaru hudu a Fadar White House.

Trump ya fara ziyarar ta sa ta jihohi biyar da yada zango a yankin Macomb na jihar Michigan, jihar da ba zato ba tsammani ya sami nasara da kuri’u 11,000 a zaben 2016 kan Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrats.

A jiya Litinin, Trump ya halarci wasu taruka biyu a Michigan, ciki har da maimaita yakin neman zabensa na karshe daga shekaru hudu da suka gabata, a wani taron gangami da aka yi cikin dare a birnin Grand Rapids, dake da mafi akasarin masu ra'ayin mazan jiya a yammacin jihar ta Michigan.

makon-karshe-na-yakin-neman-zabe-a-amukar-ya-zafafa

trump-da-biden-sun-karfafa-gwiwar-magoya-bayansu-a-jiya-lahadi

tsarin-zaben-shugaban-kasa-a-amurka

Amma zabukan jin ra’ayin masu zabe na baya-bayanan na nuna cewa Biden ne ke da fifiko a kan Trump a jihohin Michigan da Wisconsin, sai kuma mai-yiwuwa a Pennsylvania, jihohi ukun da a baya jam’iyyar Democrats suke zaba, amma Trump ya yi nasara shekaru hudu da suka gabata.

Trump da Biden sun sha ziyartar dukkanin jihohin uku, inda Trump ya gudanar da taruka hudu a Pennsylvania a ranar Asabar, shi kuma Biden ya gudanar da taruka biyu a can a ranar Lahadi.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG