Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakaken Fata Na Daga Cikin Wadanda Suka Himmatu a Zaben Amurka Na 2020


Ga 'yan kasashen Afirka da yawa da ke zaune a Amurka, ‘yancin kada kuri’a wani abu ne mai daraja. 

Ivo Tasong, ba-Amurke ne dan asalin Kamaru da yo zo Amurka a shekarar 1986, ya ce jefa kuri’a wani wabu ne da ba zai taba yin wasa da shi ba.

“Idan ka samu sa’ar zuwa Amurka da zama, wannan hakkin da ya rataya a wuyan dan kasa wato na kada kuri’a, ba zan taba yin wasa da shi ba, saboda mun san abin da iyalanmu da ‘yan uwanmu ke fuskanta a kasashenmu," abin da Tasong ya fada wa Muryar Amurka kenan.

Ya kara da cewa yanzu haka ana yaki a kasarmu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan uwanmu da yawa. Kuma matakin da gwamnati ta dauka bai iya kai ga yin sulhu cikin lumana ba don kawo karshen rikicin.

Tasong na daya daga cikin ‘yan Afrika miliyan 2.4 da aka Haifa a Amurka, kuma galibinsu sun cancanci kada kuri’a, a cewar alkaluman kidayar Amurka. Ya na da wani kamfanin fasaha a garin Silver Spring da ke jihar Maryland.

Wani sabon rahoto daga cibiyar binciken Pew da ke birnin Washington ya gano cewa bakar fata masu kada kuri’a na daga cikin wadanda suka himmatu a zaben shekarar 2020, cibiyar Pew ta kuma gano cewa tsakanin shekarar 2000 da 2018, adadin baki bakar fata masu kada kuri’a ya karu daga 800,000 zuwa miliyan 2.3.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG