NAIMEY, NIGER - A wani taron manema labaran da ya kira a birnin Yamai wakilin kamfanin Max Air a Nijar, Alhaji Boukari Sani ya bayyana cewa lokaci kawai suke jira domin a fara wannan aiki. Ya kuma yi kira ga Alhazzai da su kwantar da hankali domin a cewarsu a cikin wannan makon za a fara kwashe su zuwa gida dangane da tsarin jadawalin da hukumomin Saudia suka bayar.
Hukumar Alhazzan Nijar wato COHO a karshen wani zaman da ta yi a makon jiya ta sanar cewa kamfanin Ethiopian Airlines zai soma kwashe kason Alhazzan daga ranar 13 ga watan Yuli, yayinda Fly Nas ke sa ran fara aikin mayar da Alhazzan Nijar gida a ranar 20 ga wata.
Rashin wata tsayayyar ranar da kamfanin Max Air zai fara irin wannan aiki ya sa wasu Alhazzan Nijar suka fara tada jijiyoyin wuya har ma suka yi zanga-zanga a birnin Makkah.
Da yake maida martani wakilin kamfanin na Max Air Boukari sani ya sanar cewa tuni suka saka ranar 18 ga watan Yuli domin fara mayar do nasu kason Alhazzan Nijar gida wadanda aka kiyasta cewa sun haura 5,000.
Hutun da wani bangare na ma’aikatan tsare-tsaren Hajji suka shiga ne mafarin tsaikon da ake fuskanta wajen fara jigilar alhazzai a cewar Boukari Sani, dalili kenan ya bukaci jama’a da su kara hakuri komai zai daidaita nan ba da jimawa ba.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna