Hakan ya fito ne daga bakin jagoran tawagar likitocin dake kula da alhazai Dakta Usman Shu’aibu Galadima a zantawar sa da sashen Hausa na Muryar Amurka a wurin taron duba yadda aka gudanar da aikin hajjin na bana a Makkah.
Jagoran tawagar likitocin yace alhazai 7 sun rasa ransu ne gabanin tafiya arfa ko shiga tantunan Muna, inda 6 kuma su ka rasu bayan tafiya muna.
Dr. Galadima ya kara da cewa yawancin wadanda suka rasu a lokacin da ake gudanar aikin hajjin sune wadanda suka yi Ibadunsu a cikin rana.
Wanda yace hakan yasa suka fuskanci matsalar lafiya da suka danganci tsananin zafi da ake kira da Heat Stroke da kuma Heat Exhaustion a turance.
Dr. Galadima ya kuma bayyana cewa an samu mata masu juna biyu fiye guda 9 yayin da 2 sukayi bari 2 kuma sun haihu, inda yayi kira ga hukamar alhazai ta kasa NAHCON data tsaya tsayin daka don hana faruwar hakan nan gaba.
Daga karshe jagoran likitocin yace ba’a samu barkewar wata cuta ba sai vdai an samu wadanda sukayi fama da cutar heat stroke dake sa gangar jiki ya dauki zafin da jiki bazai iya sarrafa shi ba.
Saurari rahoton a sauti: