Malamai da sauran masu ruwa da tsaki na addinin Islama sun dage suna ta yawo sako-sako inda alhazai suke domin fadakar da su dokoki da kuma ka’idojin aikin hajji domin tabbatar da cewa sun yi aikin kamar yadda shari’a ta tanadar.
Wakilin malaman Bauchi Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, ya yi bayani kan tsayuwar Arafah inda ya ce babban kuskure ne Alhazai su rika yawo a wannan rana, ya kuma ja hankalin maniyata da su yawaita addu’o’i da neman gafara da rokon Allah Subhanahu Wa Ta’alan ya biya musu bukatunsu.
Daya daga cikin kwamitin malamai mata kuma shugabar kungiyar mata masu da’awa ta Najeriya Hajiya Rahma Musa Sani, ta ja hankalin mata maniyata kan tsarkake niyya, neman ilimi da kuma bin doka da ka’idojin aikin.
A nasu bangaren maniyatan sun bayyana halin da suke ciki da kuma irin shirin da suka yi na ibada a ranar ta Arfa, inda wasu suka bayyana cewa zusu yi addu’o’i ga iyalan su dama kasar su Najeriya.
Aikin Hajji da ke cikin rukunan Musulunci guda biyar, kan zama wajibi a kan wanda yake da hali da lafiyar gabatar da shi akalla sau daya a rayuwa.
Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar: