Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Jigilar Maniyyatan Najeriya


Jigilar alhazan hajj
Jigilar alhazan hajj

Hukumar Alhazan Najeriya ta Kammala Jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa Saudi Arabiya a ranar Asabar 24 ga wannan wata,  kwana uku kafin hawan Arafat. 

Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya Zikirullahi Kunle Hassan Ya nuna farin cikin sa na Kammala wannan jigila, ganin cewa kasar Saudiyya ta yi wa Najeriya Karin Alhazai har dubu 95 Sabanin yadda aka bayar bara. Amma duk da haka ba a bar kowa a baya ba. Zikirullahi ya ce an fara jigilar ne ranar 25 ga watan Mayu da alhazan Jihar Nasarawa su 472. An yi sahu 172 wajen kwasan alhazan.

CHAIRMAN NAHCON: ALHAJI ZIKIRULLAHI KUNLE HASSAN
CHAIRMAN NAHCON: ALHAJI ZIKIRULLAHI KUNLE HASSAN

Zikirullahi ya ce a cikin shekaru goma da suka gabata, wannan shi ne karo na farko da za a kammala Jigilar alhazai a cikin lokaci. Zikirullahi ya ce wannan abin alfahari ne a gareshi da shi da abokan aikin sa, duba da yadda aka samu wasu matsaloli da farkon Jigilar Alhazan, amma Allah ya shiga lamarin, saboda haka aka samu sa'ar Kammala Jigilar ba tare da wata matsala ba,

Shi kuwa Darekta Mai Kula da fanin gudanar da aikin Hajjin Abdullahi Magaji Hardawa ya ce ya zuwa yau hukumar ta yi Jigilar maniyyata fiye da dubu 75, Wanda idan aka hada da wadanda suka bi jiragen yawo, za a samu jimlar alhazai dubu 95.

Jigilar alhazan hajj
Jigilar alhazan hajj

Hardawa ya ce an samu matsalar bi ta kasar Sudan saboda yakin da ake yi tsakanin kasar Rasha da Yukrain, saboda haka tafiyar ta Kara tsawo, daga sa'o'i hudu da rabi da ake yi a da, yanzu sa'o'i takwas ake yi kafin a Kai Saudi Arabia, wannan bai sa Hukumar ta yi Kasa a gwiwa ba. Hardawa ya ce Hukumar ta yi aiki tukuru wajen ganin ba a bar kowa a baya ba a Jigilar Alhazan na bana.

Daya cikin Malaman da ke ayarin maniyatan Sheikh Ahmed Suleiman Ibrahim, ya yi bayani ne kan abin da ya zama wajibi ga maniyaci a wannan lokaci na aikin Hajji. Suleiman ya ce tsayuwar Arafat ita ce aikin Hajji. Wanda bai samu Arafat ba to fa sai ya nemi kudi ya sake komawa Saudiya domin yin wani aikin hajjin saboda Arafa shi ne Hajji. Wanda ya samu Arafa ya samu Hajji.

Wata sanarwa da ke dauke da sa hannun mataimakiyar Darekta a fanin wayar da Kan al'umma na Hukumar Alhazan Fatima Sanda Usara, ta ce kamfanonin jirage biyar ne suka yi Jigilar Alhazan a bana da Max Air, da Azman, da Fly Nas, da Air Peace da kuma Aero Contractors.

Saurari rahoton a sauti:

KAMMALA JIGILAR MNIYATAN HAJIN 2023
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

XS
SM
MD
LG