Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Yi Kiran Da A Tsagaita Bude Wuta A Sudan


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ke magana ya yi kaddamar da sabbin takardun Naira a Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ke magana ya yi kaddamar da sabbin takardun Naira a Abuja

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta damu matuka da yadda rikicin kasar Sudan ke ci gaba a tsakanin Sojojin Kasar (SAF) da Dakarun ‘yan sa kai na (RSF), lamarin da ya janyo mace-mace da wahala ga fararen hula mara misaltuwa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Mrs. Francisca K. Omayuli, ta yi wannan kiran.

Sanarwa ta kara da cewa rashin sauraren kiraye kirayen da kasashen duniya suka yi ga bangarorin da basa ga muciji da juna na su tsagaita bude wuta, ya dagula al’amura ga fararen hula kuma ya sa ba a iya fara kwashe su ba.

Don haka Najeriya na fata sake jaddada bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa.

A halin da ake ciki dai, Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar na tuntubar mahukuntan kasar Sudan, kuma ta hannun ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Khartoum, inda a hukumance ta gabatar da bukatar neman izinin kwashe daliban Najeriya da sauran al’ummar Najeriya da ke son barin kasar.

Bugu da kari, Ofishin Jakadancin Najeriya ya samar da hanyoyin tuntuba ta manhajojin WhatsApp da Telegram ga dalibai da sauran ‘yan Najeriya a Sudan, saboda dalilan samun hadin kai yadda ya kamata da sabbin bayanai akai-akai.

An shawarci ‘yan Najeriya mazauna kasar da su kasance a cikin gida, kuma su tuntubi Ofishin Jakadancin ta wadannan lambobi kamar haka:

+249 90 765 0702, +234 803 698 1824, +249 90 132 5359, +249 92 440 1217.

XS
SM
MD
LG