Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nakasassu Sun Bukaci a Taimaka Masu


Wasu nakasassu
Wasu nakasassu

Nakasassu a jihar Filato sun bukaci gwanatoci da kungiyoyi da daidakun jama'a kan su taimaka masu domin inganta rayuwarsu.

Nakasassun daga kananan hukumomi goma sha bakwai na jihar sun fito ne domin tunawa da ranar nakasassu da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe.

Yayin bikin tunawa dasu suka kira ga gwamnatoci da kungiyoyi da masu hannu da shuni su tallafa masu domin su more rayuwarsu da kuma samun ingantaka. Sun koka game da yadda a ka mayara dasu saniyar ware a cikin al'ummomi.

Wani Joseph Jacob Dakup ya ce wasu mutane sun dauka nakasassu suna da wata cuta ne yadda idan an yi kusa dasu za'a kamu da cutar. An daukesu kamar su ba mutane ba ne. Ya ce akwai wasu abubuwa da nakasasshe zai yi da wani mai kafa ma ba zai iya yi ba. Ya ce kodayake gwamnati na kokarin ta taimaka masu fatansu shi ne wata rana gurgu ko makaho ya zama gwamnan Filato. Ya ce a yanzun nan akwai nakasassu dake neman zama kansiloli a zabe mai zuwa.

Ezekiel Dung shugaban makafi na arewa ta tsakiya ya ce akwai 'yan kungiyarsu da yawa da suka gama makarantu iri daban daban amma babu aikin yi. Har wa yau akwai wasu ma dake da sha'awar zuwa makaranta amma babu hali. Talauci ya hanasu sayen irin kayayakin da makafi ke anfani dasu wurin koyon karatu. Gwamnati ta bada dan taimako amma suna kiran gwamnati ta kara bude hannu domin wasu su samu su yi karatu.

Uwalle Dahiru ta ce basu da komi amma duk abun da Allah ya huwacewa shugabanni su basu suna godiya.

Ganin irin mawuyacin halin da nakasassu ke ciki ya sa gwamnatin Filato ta kirkiro wata hukuma ta kula da su ta kuma kare hakinsu. Shugabar hukumar Mary Jatau ta bayyana irin kalubale da suka fuskanta da kuma nasarorin da suka samu. Hukumar ita ce ta farko a Najeriya kuma an kafa ta ne domin a samu a shigar da nakasassu cikin harkokin jihar da ma kasar. Hukumar na kula da zancen ilimi, lafiyarsu da samar masu da aiki da kuma tabbatar cewa ba'a musguna masu ba.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG