Malam Muntari Sale shi ne sakataren yada labaru na kungiyar makafin arewacin Najeriya kuma ya ce suna da matsaloli.Ya ce sun gode har Majalisar Dinkin Duniya ta tuna da nakasassu a matsayin mutane har ta ware masu rana ta musamman. To sai dai ya ce nakasassu a Najeriya suna cikin wani halin lahaula-walakawati. Dalili ke nan suka ce nakasassu su zauna gida yau su cigaba da addu'o'i domin Allah ya kawar masu da irin bala'in da suke ciki a Najeriya. Misali, ya ce yanzu akwai nakasassu da aka kulle a Buwari Abuja haka ma a birnin Legas. Kana a Kano ya ce an kwace masu makarantu.
Ire-iren wadannan matsalolin suka sa basu san idan zasu sa kansu ba. Kamata ya yi gwamnatocin arewa su yi doka cewa a inganta rayuwarsu. To amma maimakon su yi hakan sai suna dokokin da zasu kara nakasa rayuwarsu.
Bukatar nakasassun Najeriya shi ne nakasassun duniya su zo su tayasu yaki domin in ji Muntari Sale nakasassun Najeriya suna cikin wani tarko. Ya ce nakasassu su sani 'yanci ba zai yiwu ba a kan gado ko a tebur. Ba ma zai yiwu ba da lalama. Don haka dokar cewa a hana 'yan kungiyoyinsu yin bara sun yi watsi da ita. Basu yadda ba. Basa tare da irin wannan dokar domin gwamnatocin basu inganta rayuwarsu ba.
Isah Lawal Ikara nada rahoto.