Gwamnatin jihar ta bayyana cewa, tana iyaka kokarinta na tallafawa makafin yadda ya kamata. Gwamnatin ta kuma bayyana cewa, ba a ko’ina bane aka hana bara. Bisa ga cewar kwamishiniyar mata da nakasassu ta jihar, Hajiya Hassana Adamu, ana hana makafin bara a wadansu wurare ne domin kare mutuncinsu.
A cikin wani taron manema labarai da ta kira, kwamishiniyar tace an hana barace barace ne a manyan hanyoyin cikin garin Minna. Tace an ba makafin izinin zama wurare dabam dabam da suka hada da layin gidan sarkin makafi. Bisa ga cewarta, mabaratan zasu iya zama wajen gidan sarkin makafi da gidan kutare da kuma wani wuri dake Cancaga inda zasu iya zama wanda yake da niyar bada sadaka yaje ya neme su cikin mutunci.
Hajiya Hassana Adamu tace, gwamnatin jihar Naija ta kashe sama da Naira miliyan biyar wajen horas da makafi sana’oin hannu wadanda suka kamala aka basu takardun shaida da kuma kudin jari, banda haka kuma ana ci gaba da horas da wadansu a halin yanzu.
Isa Umar Aliyu shugaban hadaddiyar kungiyar makafi da ya halarci taron manema labaran yace abu daya da suke bukata a wajen gwamnatin jihar Naija a halin yanzu shine a yi masu rangwame a asibiti. Ya kuma yaba kokarin gwamnati na basu ilimi kyauta.
Wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya ruwaito cewa, gwamnatin ta maida martanin ne sakamakon korafin da kungiyar makafi tayi kan kama su da gwamnati ke yi da kuma hanasu bara ba tare da basu tallafin kirki ba.