WASHINGTON, DC —
'Yar majalisar dattijan Najeriya A'ishah Jummai Alhassan daga jihar Taraba, ta mika agajin kayan abinci tare da gurabun karo ilmi ga nakasassu a jihar, albarkacin watan azumin Ramadan.
Kayan da aka raba wa nakasassun a azumin bana, ya hada da buhu hamsin na shinkafa, da buhu hamsin na masara, da buhu hamsin na gero da kuma katon hamsin na madara.
A baya, ita wannan 'yar majalisar ta kafa cibiyar koyar da na'urorin kwamfuta, tare da samar da kekunan guragu ga nakasassu na jihar. Haka kuma, an ce tana bayar da gurabun karo ilmi ga su nakasassun, musamman a Kolejin horas da Malamai dake Jalingo.
A wani gefen kuma, matasa a Jalingo sun rungumi gudanar da ayyukan gayya, musamman na sharewa tare da gyara wuraren ibada da kuma makabarta a lokacin wannan wata na Ramadan.
Wakilin sashen Hausa, Ibrahim Abdulaziz, ya aiko da cikakken bayani.