Can baya kungiyar IZALA ta ba da taimako ma wadanda tashin tashinar 'yan Boko Haram ya rutsa da su a jihohin arewa maso gabashin kasar Najeriya a karkashin Manara.
A karkashin kungiyar ta Manara, IZALA ta fara gyara da tsaftace masallatansu da sauran wuraren da suke yin ibada.
A karkashin Manara akwai shirin tallafawa duk wanda ya ke da matsalar rashin kafa ko rashin hannu sabili da wata annoba.
Irin wadanda suka samu ciwon shan inna ko karaya da ta kai ga nakasa Manara za ta taimaka da kafofin roba ko karfe domin a tallafa masu domin rayuwarsu ta inganta su ji dadin abubuwan da suke yi tare da tafiya zuwa wuraren da suke so.
Za'a yi masu kafa ko hannu kyauta ba tare da biyan ko kwandala ba.
Wannan taimakon kowane dan Najeriya na iya samu daga kungiyar ba lallai sai ya kasance musulmi ba, inda duk aka samu mutane suka kai dari Manara za ta kawo injinan aiki da kwararru su sarafa kafafuwan da hannuwa.
Idan ma an yi hatsarin mota dan agaji zai kawo taimako ma kowa da hatsarin ya shafa ba tare da kula da kabilanci ko addini ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya