Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Corona Ya Haura Dubu 100 a Najeriya


Wani dakin kula da Masu cuter corona
Wani dakin kula da Masu cuter corona

Hukumar NCDC da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce mutanen da cutar COVID-19 ta harba a kasar, sun haura 100,000.

“Ya zuwa ranar Litinin, mutum 100,087 aka tabbatar suna dauke da cutar. Mutum 1,358 ne suka mutu.” Shafin yanar gizon NCDC ya bayyana.

Legas ce ta fi kowacce jiha yawan masu dauke da cutar da mutum 36, 101 sai Abuja mai mutum 13,448 sai Kaduna da ke biye da ita da mutum 5,801.

“Tun daga farkon watan Disamban 2020, Najeriya ke ganin karin masu dauke da cutar akai-akai.”Shafin Twitter ne NCDC ya kara da cewa.

A ranar Lahadi kadai sabbin mutum 1,024 aka samu sun kamu da cutar a jihohi daban na kasar.

Hukumar ta kuma ce ta sallami adadin mutum 80, 030 bayan da suka warke.

A dalilin haka hukumomi suke duba yiwuwar sake saka matakan kulle a duk fadin Najeriyar yayin da ake fuskantar tutsun annobar a karo na biyu, matakin da al’umar kasar da dama ke adawa da shi.

“Har yanzu ba a fita a kangin annobar COVID-19 ba amma samun allurar rigakafin cutar zai kai mu kusa da matakin dakile yaduwarta.” In ji NCDC.

Cutar ta COVID, wacce ta faro daga yankin Wuhang na kasar China a bara, ta harbi sama da mutum miliyan 90 a duk fadin duniya a cewar cibiyar kula da cutar da ke jami’ar Johns Hopkins.

Ta kuma halaka kusan mutum miliyan biyu a duniya inda cutar ta fi kamari a Amurka, wacce ta ke da mutum sama da miliyan 22 da suka kamu da ita kana sama da mutum 374 da suka mutu.

XS
SM
MD
LG