Yanzu haka dai an fara gudanar da wannan gwaji a jihohin Gombe da Enugu da Nasarawa da kuma Lagos.
Mai bada shawara na musamman ga shugaban hukumar NCDC Farfesa Ehimario Igumbor, ya ce an zabi jihohin ne domin wakiltar kowane yanki na kasar da kuma yadda jihohin keda yawan masu cutar da karancin masu ita.
Kakakin kungiyar tabbatar da tsaro da zaman lafiya a arewa Salihu Dantata, ya ce matakin abune mai kyau ganin yadda mutane su ka yi watsi da matakan kariya.
Sai dai kuma wasu yan Najeriya da masu sharhi sunyi tir da wannan matakin suna masu nuna cewa cutar batayi ta'azzarar da za a kashe wasu makudan kudade domin gwajin gida-gida ba.
Tun bayan bullar cutar a Najeriya hukumomin lafiya suke ta kokarin wayar da kan jama'a kan bin matakan kariya domin dakile yaduwarta.
Domin karin bayani saurari rahotan Hauwa Umar.
Facebook Forum