Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Fara Tilasta Sanya Takunkumin Kariya A Najeriya


Takunkumin Rufe Fuska.
Takunkumin Rufe Fuska.

Hukumomi a Najeriya sun bayyana a niyyarsu ta tabbatar da ‘yan kasar sun bi dokokin kare kai daga cutar corona, da suka hada da cin tarar kudi Naira dubu ashirin ko kuma daurin watanni shida ko kuma duka biyun muddun aka samu mutum bai sanya takunkumin fuska ba, musammm a cikin taron jama’a.

Wannan mataki da gwamnati ke son daukawa na daga cikin dokokin kasa na ganin ta kare rayukan ‘yan kasa daga duk wata annoba da za a iya yadawa ta hanyar cudanyar mutane da shiga motocin kasuwa ko kuma na mallakar mutum muddun zai fito waje ya yi mu’amala da sauran jama’a kamar kasuwanni dama sauran wurare makamantan haka.

Malam Muhammed Bello Dauda, Jami’in kiwon lafiya a Asibitin Kwararru a Bauchi, yayi Karin haske kan wannan batu da cewa lallai za a iya cewa cutar coronavirus ta dawo a mataki na biyu a cikin watan Nuwamba. Ya ce an samu mace mace a wannan mako.

Malam Bello Dauda ya kara da cewa za a fara daukar matakin cin tarar duk wanda bai sanya takunkumin ba koda a kuskure ne, ya kuma yi kira ga mutane su rika nesantar da juna a cikin matakan kare kai daga annonbar da kuma taimakawa wurin dakile yaduwan cutar.

A halin da ake ciki, Gidauniyar BUA, mallakar wani dan kasuwa mai suna Abdulsamad Isyaka Rabiu ta aiko wa gwamnatin jihar Bauchi da kyautar motocin daukar marasa lafiya da kuma dubban takunkuman rufe hanci da baki.

Alhaji Idi Hong da ya kawo kayayyakin kana ya wakilcin shugaban gidauniyar wurin bada kayan, ya ce manufar wannan taimako ita ce rage wa al’umma radadin annobar. “Kayayyakin sun hada da motocin daukar marasa lafaiya guda uku da abin rufe fuska dubu hamsin da sauran su.”

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Kauran Bauch, shi ne ya karbi kayayyakin a madadin gwamnatin jihar Bauchi. Ya kuma gode wa shugaban gidauniyar BUA, Abdulsamad Isyaka Rabiu kana ya yi alkawarin amfani da kayayykin kamar yanda gidauniyar ta bukaci a yi.

Ga dai rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG