Kwamishanan shari'a na jihar Barrister Abdullahi Bawa Wuse ya ce suna gudanar da bincike amma akwai cikas da suke fuskanta. Ya ce sun samu labarin fyaden ne ranar Laraba da ta gabata. Ya yi magana da lauyan gwamnati dake Kontagora kuma har ya dauki maganar daga hannun 'yansanda. Saidai ya ce cikas da suke samu yanzu shi ne rashin ikon yin bincike. Wannan iko ne da ya rataya a wuyan 'yansanda. Har yanzu suna kokari su samu cikakken bayani domin su san abun da zasu yi nan gaba. Ya ce sun fara gabatar da maganar gaban shari'a kamar yadda ya kamata.
Dangane da korafe-korafen rufa-rufa da uban yarinyar ya ce ana yi masa kama daga 'yansanda har likitocin dake kula da yarinyar kwamishanan ya ce zasu yi abun da yakamata da 'yansanda da likitoci har su kai ga gaskiyar maganar.
Kasancewa iyayen yarinyar talakawa ne an tambayeshi ko akwai abun da gwamnati zata yi ta taimaki yarinyar sai ya ce suna nan suna daukan mataki domin taimaka mata. Dauketa daga asibitin Kontagora zuwa wani daban ya ce ya danganta da abun da likitoci suka shaida masu. Yanzu ba zasu so su yi wani abun da za'a zargesu da yin katsalandan ga yanayin bincike ba. Duk abun da zasu yi zasu yi bisa ga umurnin masana kwararru. Suna magana da likitoci kuma sun ce zasu basu rahoto.