Sabili da wai iyayen matasan masu hannu da shuni ne wadanda suna iya yin anfani da kudi yayin da ita kuma yarinyar 'yar talakace ya sa Muryar Amurka ta bi digdigin maganar ta tabbatar da gaskiya.
Jami'in 'yansandan da Muryar Amurka ta zanta da shi ya ce matashi na biyu da suka kama shi ya fada masu gaskiya. Ya tabbatar masu cewa su uku ne suka yi fyaden. Wanda suka fara kamawa shi ya shirya aika-aikar ya kawo kwayar da suka saka cikin ruwan lemun da suka baiwa yarinyar ta sha. Ya tabbatar masu cewa zai taimakesu su kama na ukunsu. Kawo yanzu an gurfanar dashi a gaban shari'a. Yanzu yana tsare gidan kaso.
Yaron ya gayawa 'yansanda cewa kwayar da suke sha irin wadda ake ba doki ne. Ita ce suka sa a cikin lemun da suka ba yarinyar. Ta bakin 'yansandan yarinyar tana samun sauki.
Da aka fada ma jami'in 'yansandan cewa uwayen yarinyar sun yi zargin cewa za'a hada baki da su 'yansanda a yi watsi da maganar sai ya ce babu wanda ya isa ya hada baki da su. Ya ce su suna aikinsu daban da likitoci. Domin haka babu abun da ya hadasu. Wadanda suka yi laifi babu wani danuwansu ciki. Duk wanda ya yi laifi dole su bishi a hukuntashi. Ya ce kowa ya san abun da ya faru kuma za'a bi gaskiya.
Duk da nasarar da 'yansanda ke ikirarin samu mahaifin yarinyar Malam Mohammed Rabiu ya ce shi bai gamsu da yadda lamarin ke tafiya ba. Ya ce daga hukuma zuwa likitoci babu wanda ya yi masa magana ko ya ce masa ga matsalar da ya gani. Har yanzu ba'a fada masa irin maganin da ake bata ba.
Aisha yarinyar da aka yiwa fyade yanzu ta kwashe makonni biyu kwance a asibiti. Sa'adatu Abdullahi yar mahaifiyar Aisha ta shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa yanzu ana iya cewa ta soma samun sauki domin ta bude idanu, tana gani amma har yanzu bata iya magana.
Ga karin bayani.