Wasu sun yi korafi dangane da rufe wasu hanyoyi na kuasn sa'o'i biyar wai har sai shugaban ya bar birnin. Suna ganin yin hakan bai dace ba.Rufe hanyoyin zai shafi harkokin yau da kullum musamman kasuwanci. Idan an rufe hanyoyi gaba daya ina mutum zai bi ya wuce? Tamkar an cewa kowa ya zauna gida kenan. An ce duk manyan hanyoyi jami'an tsaro sun toshe babu fita babu shiga.'Yan kasuwa da aka ce su rufe shagunansu daga karfe tara na safe har sai wajen karfe biyu ko uku su bude sun ce zasu tafka asara. Ko ma'aikata ma an ce su fita da wuri.
Amma hukumomin soji sun ce sun dauki matakan ne domin tabbatar da doka da oda kamar yadda janaral Nicholas Rogers sabon kwamandan rundunar soji ta 23 dake Yola ya fada. Ya ce hanyar da ta taso daga filin saukar jirgin sama zuwa fadar Lamidon Adamawa zasu rufe. Ya ce a gayawa mutane su yi masu hakuri.
To sai dai ana musayar kalamai tsakanin 'yan APC da PDP a jihar. Shugabannin PDP a jihar suna zargin gwamnan da kasa tabuka komi domin marabtar shugaban kasar zargin da 'yan bangaren gwamnatin ke musantawa. Barrister A. T. Shehu sakataren PDP bangaren Joel Madaki ya ce gwamnatin Adamawa bata yiwa mutanen jihar komi ba. Ya ce abun kunya ne ma a ce hanyar da shugaban kasar zai bi ya shigo Yola ana ciketa da jar kasa.
Gwamnan jihar Murtala Nyako ta bakin sakataren yada labaransa Ahmad Sajoh ya ce ba haka zancen yake ba. Ya ce a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya zasu bashi goyon baya. Ya ce suna marabtarsa zuwa jihar Adamawa wadda jihar APC ce.
Shugaban yana Adamawa ne ya bude wata makarantar sakandare ta soji da aka gina kana ya ziyarci fadar Lamidon Adamawa wanda ake zaton watakila ya sa baki a dambarwar siyasa dake tsakanin shugaban kasa da gwamnan jihar.