Lamarin ya auku ne jiya lahadi sa'ilinda kasuwar kauyen take cike makil ana hada hadada.
Kwamishinan 'Yansandan jihar Borno Tanko Lawal wanda ya tabbatar da wannan labari ga wakilin Sashen Hausa dake yankin, yace maharan sun kona fiyeda rabin garin, suka raunata mutane fiyeda ashirin.
Mazauna kauyen sun shaidawa wakilinmu cewa yawan wadanda 'yan bindigan suka halaka ya haura hamsin.
Ahalin yanzu da yawa daga cikin mutanen kauyen sun fara gudu daga kauyuka dake yankin zuwa manyan alkariyu, ko su tsallaka zuwa kasashe dake makwabtaka da Najeriya.