A taron bita da kungiyar matan ta shirya mai taken gudunmawar mata Musulmi wajen hadin kan al'umma da tunkarar kalubalen karni na ashirin da daya wadda ta bayar da kasida Hajiya Rabi Abdullahi Mohammed ta karfafa mata da su nemi ilimi domin sanin madafa da tarbiyar da 'ya'yansu kasancewar yadda zamani ya taho da sarkakiya masu tarin yawa. Ta ce addini ya koyar cewa mutum ya yi ilimi kafin ya yi aiki. Idan mace ta san abun da ta keyi to duk wasu abubuwa zasu zama mai sauki a wurinta. Kuma uwa ita ce makaranta. Idan ta gyaru 'ya'yanta zasu gyaru. Idan al'umma ta lalace babu wata sauran magana. Nan da shekara talatin yaya 'ya'yanku zasu zama. Idan an yi masu tarbiyar kirki za'a samu al'umma ta gari.
Shugaban kungiyar Salman Muhammed Musa ta bayyana dalilin shirya taron bitar da kuma wasu ayyukan da kungiyar ke gudanarwa. Na daya suna murnar cika shekara ashirin da biyu da kafa kungiyar a jihar Filato.Na biyu suna kiran mata su hada kai domin su taimaki 'ya'yansu. Na uku suna kula da gidajen marayu inda suke basu abun da suka tanada masu.Suna kai agaji gidan kaso su kuma yiwa mutanen ciki nasiha bisa ga laifukan da suka kaisu gidan. Suna shiga kauyuka domin fadalkar da addinin musulunci. Suna yiwa mata nasiha kan zaman aure. Suna da shirin koyas da sana'ar hannu ga mata.