Masu shigo da kaya daga kasashen waje sun ce yawan kudin haraji da gwamnati ta sa shi ne umalubaisan matsalar da hukumar kwastan ke fuskanta dangane da haraji. Masu fatauci sun ce laifin na gwamnatin Najeriya ne. Idan bata gyara ba haka lamarin zai cigaba da kasancewa.
Babbana jami'in kwastan Isyaku Maitama Kura mai kula da jihohin Kogi da Kwara da Neja ya bayyana matakan da suke dauka domin magance matsalar musamman ga masu sana'ar shigo da motocin takunbo. Ya ce kullum suna kirawo masu fataucin tsoffin motoci su zo su gaya masa duk abun da suke so hukumar kuma zata yi masu. Ya ce sun rokesu su fada masu zasu taimakesu amma su rika yin gaskiya. Su daina neman wasu mutane su yi masu takardun haraji na bogi. Ya ce idan jami'in kwastan ya tsayar da mota ya tambayi takardun haraji da sun sa cikin naurarsu sasu sani ko takardar bogi ce ko ta gaskiya.
Dangane da kama masu wannan danyen aikin sai Malam Isyaku ya ce wata kungiyar kunci ce kuma suna kokarin kama mutanen.
Alhaji Sani Ragada daya daga cikin shugabannin masu sana'ar shigo da motocin takunbo ya ce tsadar kudin harajin ya yi yawa shi ne dalilin samarda takardun haraji na bogi. Ya ce kudin da suke biya da yanzu ya ninka biyu. Misali da kan motar nera miliyan daya harajin nera dubu dari da ashirin suke biya amma yanzu suna biyan dubu dari biyu da arba'in. Ya ce karin da gwamnati ta yi ya wuce kima. Shi ma Alhaji Mustapha Osto wani dan kasuwa dake shigo da kaya ya ce gaskiya suna cikin matsala. Idan mutum ya shigo da kaya sai ya ga bai samu ribar da taka kara ta karya ba sabili da dimbin haraji da aka sa ma kayan.Ya kira ga gwamnati ta sawakawa mutane kudin harajin.
Sai dai hukumar kwastan ta ce biyan harajin ya fi takardun bogin domin da kudin harajin ake yiwa kasa aiki.Babban jami'in kwastan din Isyaku Maitama Kura ya kira 'yan kasuwa su mutunta kasar. Ya ce kudin da suke tarawa ba aljihunsu suke shiga ba. Na gwamnati ne.