Bisa ga tsarin za'a yi zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar ranar 14 ga watan Fabrairun 2015 yayin da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jihohi zai biyo baya ranar 20 ga watan Fabrairun.
Tuni 'yan siyasa suka soma yin tsokaci kan jadawalin a jihar Kano. Mukhtari Yakubu Farisa ya ce a tashi fahimtar tsari ne da ba zai cutar da kowane bangare ba. Idan an bi tsarin za'a yi zabe cikin kwanciyar hankali da samun ingantattun shugabanni.Wani kuma cewa yakamata a hade zabukan a yisu rana daya. Idan an yi haka cikin mako daya an san sakamako maimakon a rarraba
Ismail Abdullahi Kwalwa mai sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya ya ce jadawalin zaben abun ne kamar an yiwa 'yan siyasa adalci domin an basu lokaci mai tsawo daga yanzu zuwa watan goma na wannan shekara zasu gama duk abun da ya kamata su yi na fitar da 'yan takara kana a shiga ruguntsimin zabe daga watan goma zuwa Fabrairu na shekara mai zuwa. Amma ya ce inda matsalar take shi ne yadda aka shirya a fara da zaben shugaban kasa da majalisun kasa kana bayan mako daya a yi na gwamnoni da majalisun jihohi. Ya ce wannan ba abu ne wanda zai yiwa tsarin zaben daidai ba. Idan ana son a taimakawa kasar ko a yi zabukan rana daya ko kuma a fara da na gwamnoni da majalisun jihohi daga baya a yi na shugaban kasa da majalisun tarayya.
Sanato Ibrahim Kabiru Gaya daga Kano ya ce su a shawararsu a majalisar dattawan kasar shi ne a yi zabe rana daya. Ya ce kuma zasu yi gyara su tabbatar da yin hakan. Da aka jawo hankalinsa bisa ga dokar da INEC ta dogara a kai sai ya ce kowace doka ce zasu gyara domin su suka yi dokar.