Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alama Boko Haram Na Bukatar Kungiyoyi Su Shiga Tsakaninta da Gwamnati


Wani shugaban Boko Haram tare da wasu 'yan matan Chibok da har yanzu suke hannusu
Wani shugaban Boko Haram tare da wasu 'yan matan Chibok da har yanzu suke hannusu

Labarin a musayar 'yan Boko Haram dake gidajen yari domin sako 'yan matan Chibok ya nuna Boko Harama din na bukatar shiga tsakanin kungiyoyin da zasu amince dasu domin samun mayakan nasu.

An taba irin wannan yunkuri a zamanin gwamnati shugaba Goodluck Jonathan har kowa ya sa rai za'a sako 'yan matan amma bisa ga wasu dalilai da har gobe kasar bata sani ba sai yunkurin ya wargaje.

Ganin bidiyon da wani bangaren Boko Haram ya fitar tare da wasu cikin 'yan matan har ma da sa daya daga cikinsu tana kiran gwamnati ta dauki duk matakan da suka dace domin a sakosu, ya tada kaimin masu ruwa da tsaki ta wannan bangaren.

Wasu mayakan Boko Haram
Wasu mayakan Boko Haram

Shugabar kungiyar hana kangarewar matasa Halima Baba Ahmed na ganin za'a samu nasarar fitar da matan ta wannan hanya. Tace Boko Haram tayi hakan ne domin da an taba yin hakan amma haka bai cimma ruwa ba ya sa take son wata kungiya ta shigo tsakaninta da gwamnati. Idan har an samu kungiyar da ta shiga tsakani za'a ci nasara.

To saidai wani masanin harkokin tsaro Dr.Muhammad Bello na jami'ar Jigawa yace bin wannan hanya ba mai bullewa ba ce. Yace a duk duniya wa zai fito yace zai taimakawa wani dan ta'ada. Yace kasashe kamar su Amurka, Birtaniya, Faransa da makamantansu basa yi. Yace duk wadanda suke fitowa suna cewa sun sansu karye su keyi.

Dr. Bello yace 'yan Boko Haram ba 'ya'yan goyo ba ne. Mayaudara ne, su yaudari mutane, su yaudari gwamnati kana su cigaba da ta'asa. Yace an sha yi dasu amma babu abun da aka samu.

Akan a yi musayar firsinoni domin 'yan ta'adan su sako 'yan matan Chibok, Dr Bello yace an san wadanda ake tsare dasu amma babu wanda ya san wadanda suke yaki a daji. Idan ba'a yi hattara ba wani kuskure za'a sake tafkawa.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG