Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan CBN Ya Ce Bayan Dauri A Kwace Dukiyar Sata


Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi

Mukaddashin gwamnan jahar Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje Ya gabatarwa Sanusi Lamido Sanusi damuwar su game da barayin dukiyar kasar Najeriya.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Malam Sanusi Lamido Sanusi yace ya kamata a kwace kudade da kadarorin sata daga hannayen jami'an gwamnati da suka saci dukiyar al'umma. Sanusi Lamido Sanusi, ya fadi haka ne a lokacin da yake maida martani bayan da mukaddashin gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kara jaddadawa gwamnan Babban Bankin cewa 'yan siyasar Najeriya su kan saci kudin Najeriya su kai kasashen waje su sayi dukiyoyi a kasashen waje amma kuma idan maganar ta fito fili gwamnati ba ta yin kokarin da ya kamata ta yi maganin abun.

Dr.Abdullahi Umar Ganduje ya ce, wannan ya na shafar matsayin Najeriya saboda sanadiyar hakan ne ya saka kasar a cikin jerin kasashen duniya da suka yi nisa a kan karbar rashawa, sannan yayi kira ga Babban Bankin Najeriya wato CBN, da Ma’aikatar kudi ta Najeriya su gaggauta karbo kudaden gwamnati da ake zargin tsohon shugaban Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha da sacewa ya kai su ajiya kasashen waje.

Mukaddashin gwamnan na jahar Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje ya ce da irin kudaden nan na sata ake yin amfani ana sayen talakawa kuma ana gurbata demokradiya a Najeriya. Wakilin Sashen Hausa a jahar Kano , Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana da karin bayani kamar haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG