Wasu mutanen da suka kubuta da rayukansu tare da shaidu a kusa da wurin sun ce an tsinci gawarwakin mutane 19, cikinsu har da wasu direbobin manyan motoci biyu, a wurin da 'yan bindigar suka yi kwanton-bauna a kusa da garin Logumani, kimanin kilomita 30 daga bakin iyaka da Kamaru.
Shugaban wata kungiyar banga fararen hula mai tallafawa gwamnati a yaki da 'yan Boko Haram, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa biyar daga cikin mutanen an harbe su ne da bindiga, sauran 14 kuma yanka su aka yi.
Wasu rahotannin sun ambaci shaidu da wadanda suka kubuta da rayukansu su na fadin cewa 'yan bindigar sun daina kashe mutane ne kawai suka gudu a kan babura abayan da daya daga cikinsu ya samu kira a waya, watakila ko an fada musu cewar ga jami'an tsaro tafe ne.
Wani mutum guda ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa har an fito da shi daga cikin mota za a kashe shi, sai wayar dan bindigar ta buga, kuma da ya amsa sai suka hau babura shi da sauran 'yan bindigar suka gudu.
Yace sun cinna wuta ma motoci guda biyar a wurin kafin su gudu.