Dan majalisar yayi wannan furuci ne a yayin tattaunawar shi da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a birnin Maiduguri, Haruna Dauda Biu. Sanata Ali Mohammed Ndume ya ci gaba da cewa ta hanyar gyara kundin tsarin mulkin kasa ne kawai za a iya tabo duka irin wadannan matsaloli amma ba kamar yadda shugaban kasar yayi ba ta hanyar zabo mutane goma sha uku kawai daga cikin jahohin kasar talatin da shida, har da Abuja babban birnin tarayya.
Sanatan ya ce mutanen nan goma sha uku da shugban ya zabo ba za su iya sanin illahirin matsalolin da kasar Najeriya ke fama da su ba. Sannan ya ci gaba yin bayani kamar haka: