A lokacin da yake magana a Yola, hedkwatar jihar Adamawa, shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, Mu'azu babangida Aliyu, ya musanta tunanin da wasu ke bazawa cewa 'yan yankin arewacin Najeriya ne suke shakka, kuma ba su son a zauna a yi taro na kasa a Najeriya.
Gwamna Aliyu ya shawarci al'ummar arewa da su zabi wakilai na kwarai da zasu wakilce su a zauren taron ba tare da tsoron komai ba, yana mai fadin cewa ai babu abinda Arewa ke son gani illa ci gaba da bunkasar Najeriya.
Wasu manazarta irinsu Daniel Madu Bwala, Talban Adamawa, su na masu ra'ayin cewa tilas a hada da sarakunan gargajiya idan ana son samun nasarar wannan taro na kasa da ake magana a kai.